
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hespress cewa, taron wanada yana daga cikin irinsa d ake gudanarwa a kasar, zai samu halartar baki daga koina a sassa na kasashen larabawa da na musulmi, wanda a za agudanar a jami’ar Sidi Muhammad Bin Abdullah.
Babban abin da za a mayar da hankalia akansa shi ne bangaren gajiyarwa irion ta kur’ani mai tsarki, da kuma matsayin sunna a bangaren bayanin kr’ani.
Daga cikin kasashen da za su tura wakilansu har da kasashen Saudiyya, Masar, Algeria, Kuwait, UAE, da kuma Iraki da dai sauransu,wadanda dukkaninsu mambobi ne a cibiyar da ke kula da tarukar mujizar kur’ani ta duniya.
Wannan taro dai ana gudanar da shit un bayan da aka kafa cibiyar ta kasa, kuma ana canja ksashen da ke daukar nauyinsa, inda a shekara mai zuwa kuma za abayyana kasar da za ta dauki nauyin gudaar da shi.
Kasshen musulmi dai suna bayar da muhimamnci ga wannan taro, domin kuwa ya kunshi bangarori daban-daban na ilmantarwa da kuma darussa masu muhimamnci na kur’ani.