IQNA

An Bude Wani Kamfe Na Neman A Saki Sheikh Zakzaky A Birtaniya

23:45 - April 21, 2016
1
Lambar Labari: 3480343
Bangaren kasa da kasa, an bude wani kamfe wanda kungiyoyin kare hakkin bil adama akasar Birtaniya suka fara da nufin a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Kamfanin dillanicin labaran Iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV cewa, wasu masu rajin kare hakkin bil adama a kasar Birtaniya sun fara kamfe na neman a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran harkar muslunci a Najeriya da gwamnatin Najeriya take rike da shi.

Masu fafutukar dai sun nuna rashin gamsuwarsu da ci gaba da rike malamin da gwamnatin najeriya take yi ba tare da gurfanar da shia gaban shari’a ba.

Wannan mataki dai ya zo tun bayan da rundunar sojin Najeriya ta yi amfani da karfi kan fararen hula marassa makami tare da kashe daruruwa masu daga cikinsu a karshen shekarar da ta gabata, ba tare da bayyana wata hujja wadda ta yi daidai da abin da suka aikata ba..

Wannan lamari ya sanya masu bin diddidin lamarin gami da kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasashen duniya daban-daban yin fargaban cewa, mai yiwuwa gwamnatin Najeriya na hankoron ganin bayan mabiya mazhabar shi’a mabiya harkar musulunci a kasar.

3490843

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 2
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Muhammad ishaq gzw
0
1
Free zakzaky
captcha