
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Hubbaren Imam Ali (AS) cewa, wannam shi ne karon farko da ake gudanar da irin wannan shirin wanda ya kunshi mata zalla.
Kimanin mata 100 ne shirin ya kunsa, wadanda suke gudanar da hardar kur’ani mai tsarki kama daga izihi na 1 zuwa na 3 da kuma 5 har zuwa karshen gasar.
Rabab Nazar ita ce shugabar cibiyar Alkauthar wadda ta kebanci harkokin addini da suka danganmci mata a karashin wannan hubbare mai tsarki, ta bayyana cewa shirin ya samu karbuwa matuka.
Daga cikin muhimamn abubuwan da ake son cimmawa awannan shiri har da kara karfafa gwaiwar mata gudanar da lamurra da suka danganci addini musamman abin da ya shafi kur’ani mai tsarki.
A mafi yawan lokta dai aka mayar da mata saniyar ware a cikin harkoki da suka shafi kur’ani musaman ta fuskar gudanar da gasa a bangarrorin tilawa da harda da sauransu, wanda kuma su ma suna gudunmawar da za su iya bayarwa ta wannan fuska.
Hubbaren mai tsarki dai yan shirya taruka a bangarori da suka danganci kur’ani, kuma wannan shi ne karon farko da aka shirya gasar da ta kebanci mata kawai a karshin shirin kur’ani na cibiyar.