
Kamfanin dilalnicn labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na tashar Alalam cewa, Yusuf Qardawi ya samu hanyar yanar gizo ta Facebook da Twitter a matsayin hanya mafi sauki gare shi fiye da munbarin wa’azi, inda a nan ne yanzu yake baje kolin fatawoyinsa.
Yusuf Qardawi wanda ya saba fitar da fatawoyi da ke shan martini daga malamai da kuma sauran al’ummar musulmi, a wannan karon ma ya yi wata Magana wadda ya jefa kansa a cikin abin da ta kunsa kai tsaye, inda y ace mafi hadari ga malamai shi ne su bayar da fatawa bisa son ransu ko kuma bisa son ran mahukuntan da suke karkashinsu.
Da dama daga cikin masu binsa a shafukan yanar gizo sun yi ta mayar masa da martini, inda suke cewa to ai shi ne utumum na farko dawannan fatawa tasa ta shafa.
Dag acikin masu bin shafi wani yace: kai sheikh! Me akake yi ne Qatar? Shin ba kana bin sarki ba ne kana bayar da fatawa daidi abin da ransa ke so?
Yayin da kuma wani ya ce to ai sai ka gaya ma iyalan Ali Thani da ke yi musu barkwanci da sunan malamanta.