
Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «memeburn» cewa, an fara wannan kamfe ne sakamakon matsalolin da akefuskanta na ‘yan gudun hijira daga nahiyoyin Asiya da Afirka zuwa turai.
Bayanin ya ce wasu daga wadanda ba musulmi suna yin amfani da abin da ake nuna musu kan muslunci a kan cewa addini ne na ta’addanci, saboda haka suna gudun duk wani abin da zai hada su da musulmi.
Wannan kamfe ana gudanar da shi ne ta hanyoyi daban-daban da suka dace da zamani da kuma hanyoyin yanar gizo, inda akan nuna hotuna da kuma wasu fina-finai da suke nuna musulmi da kuma muslunci na hakika.
Ko shakka bab muslunci na hakika shi ne wanda yake kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai da al’ummoi da kuma wayar musu da kai kan manufarsa ta hanyar hankali da hujja.
Ayyukan ta’addanci da ake gudanarwa a halin yanzu da sunan addini da kuma goyon bayan wasu manyan kasshen larabawa da suka bayyana kansu a matsayin shugabannin musulmi, shi ne babban aibun da aka danganta da muslunci wanda goge shi ba bu ne mai sauki ba cikin kwakwalen al’ummomin duniya da dama.
Musulmin da suka fara aiwatar da wannan shiri akasar Afirka ta kudu sun gurin ganin sun cimma nasara ta hanyar fadakar da sauran mutane wadanda ba musulmi su wayar musu da kansu kan muslunci da koyarwarsa ta gaskiya.