Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «India New England» cewa, a yau ake shirin fara gudanar da wani zaman karawa jna sani a jahar Massachusetts ta kasar Amurka kan mahangar kur’ani ta baki daya tare da halartar masana.
Babbar manufar shirin dai ita ce wayar da kai kan hakinanin koyarwar kur’ani.
Daga cikin muhimman abubuwan da shirin zai kunsa, baya ga laccoci, akwai bayanai da kuma amsa tambayoyi kan addinin muslunci da kur’ani.
Wasu da dama daga cikin mutanen kasar dai suna mummuanr fahimta kan addinin muslunci, musamman ma yadda wasu ek hankoron yada akidar kiyayya da musulunci a wannan lokaci a cikin kasashen turai saboda ayyukan ta’addanci.
N fara wannan shiri ne a cikin wannan shekara ta 2016 kuma za a gudanar da shi a birane kimanin 60 daga biranan kasar ta Amurka.