IQNA

Kididdigar Da Ake Bayarwa Kan Kyamar Musulmi Bata Bayyana Hakika

23:30 - April 24, 2016
Lambar Labari: 3480354
Bangaren kasa da kasa, duk da karuwqar ayyukan kyamar muslmi da ke karuwava cikin kasashen yammacin turai da kuma rahotannin da ake bayarwa kan hakan, amma ba a bayyana hakikanin abin da kefaruwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Express Tribune cewa, a cikin shekara ta 2012 zuwa 2014 an samu karuwar kyamar musulmi a Canada inda hatta jami’an tsaro sun shiga ciki, kamar a Amurka tun a cikin 2000 aka fara samun wannan matsala.

Bayanin ya ci gaba da cewa bababna bin takaici yadda wannan lamari ya zama ruwan darea cikin kasashen yammacin turai, musamman tun bayan da aka fara samun kai hare-hare a cikin wadannan kasashe.

Haka na kuma musulmi a kowane lokaci su ne kan gaba wajen nuna kyamarsu kana bin da ake na ta’addanci tare da nisanta kansu da masu aikata irin wadannan abubuwa na dabbanci, amma duk da haka bas u tsira, alhali su ne suka zama ragon layya a hannun yan ta’adda a duniya.

Ana bayar da rahotanni kan abubuwan ad suke faruwa kan suulmi amma ko kadan hakan baya bayyana hakikanin abin da ke faruwa a kan musulmi, wanda wani bangarensa ne kawai ake fada.

Babban abin da ya jawo hakan kuwa shi ne, musullmi da dama suna ganin cewa bayyana abin da ake yi musu ga mahukunta bas hi da wani amfani kotasiri na bin hakkokinsu.

Babban abin takaicin da ya jawo hakan kuwa shi ne yadda wasu daga cikin mahukuntan kasashen turan ne suke halasta abin da ak eyi ma musulmi na cin zarafi.

3491491

captcha