IQNA

Jagoran Juyin Islama:

Kasashe Masu 'Yancin Siyasa Dole Ne Hada Karfi Domin kalubalantar Masu Girman kai

17:51 - April 26, 2016
Lambar Labari: 3480355
Kasashe Masu 'Yancin Siyasa Dole Ne Hada Karfi Domin kalubalantar Masu Girman kai
Bangaren kasa da kasa,a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Afirka ta kudu jagoran juyin juya halin muslunci ya bayyan acewa wajibi ne kan dukkanin kasashe masu yancin siyasa da su yi tsayin daka domin taka birki ga masu girman kai na duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarat cewa ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yammacin yau Lahadi ne, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaban kasar Afirka ta Kudu, Mr. Jacob Zuma da ‘yan tawagarsa da suka kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke birnin Tehran inda yayin da yake jaddada wajibcin kara karfafa alaka da aiki tare da ke tsakanin kasashen biyu a fagagen tattalin arziki da siyasa, Jagoran ya bayyana cewar: Wajibi ne ‘yantattun kasashen duniya su kara kusatar junansu da kuma kara karfafa alakar da ke tsakaninsu duk kuwa da kafar ungulun da wasu ma'abota girman kan duniya suke yi.

Yayin da yake ishara da katse alaka da gwamnatin nuna wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a farko farkon nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Kusan lokaci guda Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta katse alakarta da haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma gwamnatin nuna wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da irin rawar da marigayi Nelson Mandela ya taka wajen kawo karshen gwamnatin nuna wariyar launin fata ta Afirka ta kudu da kuma tsohuwar alakar da ke tsakaninsa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Gwagwarmaya da ci gaba da tsayin dakan Mandela da mutanen Afirka ta Kudu ne ya kawo karshen wancan gwamnatin zalunci mai take hakkokin bil'adama, wanda wannan aiki na Mandela ya kara sanya sabon ruhi da kuma karfafa gwiwan gwagwarmaya a dukkanin nahiyar Afirka.

Jagoran ya bayyana mahangar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da kasar Afirka ta Kudu a matsayin wata mahanga ce mai kyau da ke cike da fata, don haka sai ya ce: Lalle alakar da ke tsakanin Iran da Afirka ta Kudu wata alaka ce mai kyaun gaske sannan kuma aiki tare da hadin gwiwan da ake samu tsakanin kasashen biyu a cibiyoyin kasa da kasa wani lamari ne mai tasirin gaske. To amma duk da haka wajibi ne a karfafa irin alaka ta kasuwanci da tattalin arziki da ke tsakanin kasashen biyu daidai da irin damar da ake da ita.

Ayatullah Khamenei ya bayyana alaka da aiki tare da ke tsakanin kasashen biyu a kungiyar ‘yan ba ruwanmu a matsayin wani fagen da kasashen biyu za su ci gaba da karfafa alakar da ke tsakaninsu inda ya ce: Lalle wannan aiki tare wani lamari ne da zai amfani dukkanin kasashen kungiyar ‘yan ba ruwanmun.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Amfanin ‘yantattun kasashen duniya yana cikin kara karfafa alaka da aiki tare a tsakaninsu a fagage daban-daban ne, sannan kuma wajibi ne a yi fada da wasu turakan da ke kawo cikas da irin wadannan alakoki da wasu manyan kasashen duniya suke kafawa.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Afirka ta Kudu, Mr. Jacob Zuma, wanda shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani yake wa jagoranci, ya jinjinawa irin goyon bayan da Iran ta ba wa al'ummar kasar a fadar da ta yi da wariyar launin fata inda ya ce: Ko shakka babu al'ummar Afirka ta Kudu ba za su taba mancewa da irin wadannan goyon bayan ba, wanda ziyarar da Nelson Mandela ya kawo Iran don nuna irin wannan jinjinawa da kuma godiya a aikace ga irin wadannan goyon bayan ne.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewar kasarsa ta kasance tana adawa da takunkumin da kasashen yammaci suka sanya wa Iran, shugaba Zuma ya bayyana cewar: Lalle akwai fagage masu yawa da za a iya karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu. A saboda haka za mu iyakacin kokarinmu wajen share fagen bude wani sabon shafi na karfafa alaka ta tattalin arziki da kasuwanci (tsakanin Iran da Afirka ta Kudu).

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci dangane da wajibcin alaka tsakanin ‘yantattun kasashen duniya, shugaban kasar Afirka ta Kudun ya bayyana cewar: Wasu manyan kasashen duniya, ta hanyar fakewa da wasu batutuwa marasa tushe, suna kokari wajen hana kyautatuwar alaka tsakanin ‘yantattun kasashen duniya. To amma ta hanyar hadin gwiwa da aiki tare cikin batutuwa na duniya, lalle za mu iya magance da dama daga cikin matsalolin da ake fuskanta.

Mr. Zuma ya bayyana kokari wajen sauya tsarin Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kwamitin Tsaron Majalisar a matsayin daya daga cikin fagagen da za a iya aiki taren don haka sai ya ce: Kasashe membobin kwamitin tsaron suna amfani da wasu tsare-tsare da ke gudanar da wannan kwamitin wadanda ba su dace ba, sannan kuma ba tare da la'akari da abin da al'ummomin duniya suke so da kuma kudurin da aka kada a babban zauren majalisar dinkin duniyan ba, wajen cutar da sauran kasashen duniya.

Shugaban kasar Afirka ta kudun ya jinjinawa irin tunani da kuma gwagwarmayar Jagoran juyin juya halin Musulunci da kuma al'ummar Iran inda ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta tabbatar wa da duniya cewa lalle za ta iya magance matsalolin da take fuskanta ta hanyar dogaro da kanta, da kuma zama abin koyi ga kowa.

3491746

captcha