IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Tartili A Karbala

23:44 - April 27, 2016
Lambar Labari: 3480358
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatun kur'ania bangaen tartili a hubbaren Karbala mai tsarki.

mafanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama'a na hubbaren Hussain cewa hubbaren ne ya dauki nauyin gasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wanann gasa tana zuwa ne karkashin shirin nan na gasar kur'ani a babban dakin taro na Sayyidul Ausiya a hubbaren Imam Hussain (AS).

Wannan gasa na daga cikin irinta da ake gudanarwa a kasar wadda ke samun halartar makaranta daga sassa na kasar.

An bayar da lambobin wayar tarho ga masu bukatar yin rijistar sunayensu domin shiga cikin shirin kamar haka.

009647801188333 ko kuma 00964772656661

3492647

captcha