
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoli cewa, tare da hadin gwiwa da Majalisar dinkin duniya OIC za ta gudanar da zaman taron kan Quds a Senegal a watan gobe.
A wannan taro dai za a gayyaci masana daga sassa na kasashen duniya domin domin gabatar da makaloli da laccoci a gaban taron, wadanda za a raba daga bisani a kasashen musulmi.
Babbar manufar taron dai ita ce yin bahasi kan halin da ake ciki a birnin Quds mai alfarma, da kuma irin cin zarafin da al’ummar musulmi na palastinu suke fuskanta daga yahudawan sahyuniya, da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki da suke yi.
A shekarar da ta gabata kungiyar kasashen musulmi ta shirya wani taro makamancin wannan a birnin Jakarta na kasar Indonesia.