
Kamfanin dillanicn labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar kasar Qatar ta Al-rayah cewa, an gudanar da taron mai taken bata muslunci a kafofin yada labaran turai, a birnin Doha na kasar Qatar.
Wadanda suka halarci taron sun gabatar da jawabai da ke nuna irin babban tasirin da ke tatatre da bata sunan musulunci da kafofin yada labarai na kasashen turai ke yi.
Daga masu jawaban akwai wadanda suka yi ishara da cewa, ko shakka babu kyamar muslunci da musulmi a cikin kasashen turai ta karu matuka a cikin yan shekarun baya-bayan nan, sakamakon abin da ake fada kan addinin muslunci a kafofin yada labaran wadannan kasashe.
Muhammad Hamid Al-ahmari, shi ne shugaban cibiyar aladu ta kasar Qatar, ya bayyana cewa, abin ake fada a wadannan kafofin yada labarai, ya haifar da mummunar kyma kan musulunci a cikin nahiyar trai, kuma lamarin bai takaita nan ba kawai, yah afar da akidar tsatsauran ra’ayin kin musulunci.
Ya ci gaba da cewa alhali kuwa addinin muslunci sabanin ain da suke zato ne, domin kuwa shi addini ne zaman lafiya da fahimtar juna, ba ta’addanci ba kamar yadda suke siffanta shi.
Daga cikin kasashen da suka halarta akwai Iraki, Tunusia, Algeria, Argentina, Amurka da sauransu.