IQNA

Jagoran Juyi:

Amurka Na Nuna Tana Bin Ka'ida A Mu'amala Da Iran Amma A Aikace Ba Haka Ba Ne

23:18 - April 30, 2016
Lambar Labari: 3480367
Bangaren Siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubban ma'aikatan Iran don tunawa da ranar ma'aikata ya kuma jinjinawa sadaukarwa da tsayin dakan da wadannan ma'aikata suka yi wajen goyon bayan juyin juya halin muslnci.

A safiyar yau Laraba ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubban ma'aikatan Iran don tunawa da ranar ma'aikata inda yayin da yake jinjinawa irin sadaukarwa da tsayin dakan da ma'aikata suka yi wajen goyon bayan juyin juya hali da kuma gwamnatin Musulunci ta Iran inda ya jaddada wajibcin "magance matsalolin da ma'aikata suke fuskanta", "karfafa irin abubuwan da ake samarwa a cikin gida", "wajibcin fada fasa kwabrin kayayyaki" da kuma "haramta shigo da kayayyakin da ake da irin su a Iran". Har ila yau kuma yayin da yake ishara da ci gaba da kiyayyar da Amurka take yi da Iran, Jagoran ya bayyana cewar: Amurkawa dai ba abin yarda ba ne. Don kuwa ta hanyar ci gaba da sanya wa Iran takunkumi kala-kala da kuma haifar da yanayi na kyamar Iran, a aikace suna kafar ungulu ne ga mu'amala ta kasuwanci da tattalin arziki da Iran za ta yi da kasashen waje.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da zagaye na biyu na zaben ‘yan majalisar shawarar Musulunci ta Iran da za a gudanar a nan gaba, Jagoran ya kirayi dukkanin wadanda suka cancanci kada kuri'arsu da su fito kwansu da kwarkwatarsu don kada kuri'ar tasu.

Har ila yau kuma yayin da ya ke bayyana godiyarsa dangane da kokari da ma'aikatan kasar Iran suke yi wajen ciyar da kasar gaba, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Duk wani ma'aikaci a kasar nan, ciki kuwa har da jami'in gwamnati, minista, malamin jami'a, daliban jami'a da daliban makarantun addini, daraktoci da sauransu, dukkanin wadannan ma'aikata ne da suke samar da abubuwan masu kima da ake bukata.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewar a mahangar Musulunci, rashin aiki yi, ragwantaka da zaman kasha wando, wasu abubuwa ne da suka yi hannun riga da abubuwa masu kima, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wajibi ne dukkanin wadanda suke gudanar da ayyuka a fagage daban-daban, baya ga kokari wajen kyautata yanayin aiki, haka nan kuma wajibi ne su ba wa wannan aikin hakkinsa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Duk wani da ya ke da wani matsayi ko nauyi a wuyansa, to wajibi ne ya ba da dukkanin karfi da iyawarsa wajen sauke wannan nauyi da ke wuyansa.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin sadaukarwa da goyon bayan da ma'aikata suka ba wa juyin juya halin Musulunci da kuma gwamnatin Musulunci ta Iran tsawon shekaru 37 da suka gabata, Jagoran ya bayyana cewar: Duk da irin matsaloli na rayuwa da ake da su, amma babu wani lokaci da ma'aikata suka mika kai ga irin farfagandar da makiya suke yi a kan wannan juyin, sannan kuma ba su yi fito na fito da wannan gwamnatin ba, face a koda yaushe sun kasance masu goyon baya da kuma ba da kariya ga tsarin Musulunci.

Haka nan kuma yayin da yake mika godiyarsa ga ma'aikatan na Iran sakamakon irin sadaukarwa da basirar da suka nuna wajen goyon bayan juyin juya hali da kuma gwamnatin Musulunci, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da batun ‘nauyin da ke wuyan ma'aikata, cibiyoyin tattalin arziki da kuma jami'an da nauyin aiwatar da siyasar tattalin arziki na dogaro da kai, inda ya bayyana cewar: Babban sakon da ke cikin (taken wannan shekarar na) "Tattalin arziki na dogaro da kai..." shi ne cewa wajibi ne jami'an gwamnati su aiwatar da dukkanin bangarorin da ke cikin siyasa tattalin arziki na dogaro da kai na gaba daya.

Haka nan dangane da irin rawar da ma'aikata za su taka wajen aiwatar da siyasar tattalin arziki na dogaro da kai, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Babban nauyin da ke wuyan ma'aikata a wannan fagen, shi ne aiwatar da aiki yadda ya kamata sannan kuma da dukkan karfi da kwarewa.

Har ila yau kuma yayin da yake jaddada wajibcin kyautata yanayin aiki, Jagoran cewa yayi: Daya daga cikin batutuwa masu muhimmanci a fagen kyautata yanayin aiki da abin da ake samarwa, shi ne batun kyautata irin kwarewar da ake da ita a fagen aiki da kuma su kansu ma'aikatan, wanda nauyin da ke wuyan gwamnati a wannan fagen a fili yake.

Jagoran ya bayyana tabbatar da tsaron ma'aikata da yanayin aikinsu a matsayin daya daga cikin batutuwa masu tasiri da muhimmanci wajen karfafaf yanayin aiki inda ya ce: Lamuni da tsaron rayuwar ma'aikata suna wuyan jami'an gwamnati da wadanda suka dauke su aiki ne.

Ayatullah Khamenei ya bayyana rufe kamfanoni a matsayin daya daga cikin manyan bala'oi inda ya ce: A wasu lokuta a kan rufe kamfanoni sakamakon rashin karfi ko kuma lalacewar kayayyakin aiki da sauransu wanda a irin wannan yanayin ba za a iya cewa mai kamfanin ya gaza ba, wanda a nan wajibi ne jami'an da abin ya shafa a bangarorin masana'antu, kasuwanci, bankuna da sauransu su yi iyakacin abin da za su iya wajen magance hakan.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Koda yake a wasu wajajen gazawar masu kamfanonin ne, ta hanyar amfani da irin basussukan da aka ba su a wasu wajaje na daban da suka hada da gine-gine da sauransu, ya kan haifar da rufe su, wanda a irin wannan yanayin wajibi ne ma'aikatar shari'a, gwamnati da ma'aikatar tattaro bayanan sirri su dauki matakan da suka dace.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi Karin haske dangane da hakkokin ‘yan kwangila da masu daukar ma'aikata inda ya ce: A mahangar Musulunci ma'aikaci da wanda ya dauke shi aiki masu taimakon juna ne, ba wai makiya da abokan fada da juna ba ne.

Ayatullah Khamenei ya bayyana godiyarsa ga ‘yan kasuwar da suke amfani da dukiyarsu wajen kafa kamfanoni don samar da abubuwan da ake bukata inda ya bayyana "aiki tare cikin girmama juna tsakanin ma'aikaci da wanda ya dauke shi aiki" "kokarin jami'ai wajen saukake hanyoyin zuba jari a bangarori daban-daban" da kuma "share fagen fitar da kaya waje da kare hakkokin masu fitar da kaya waje" a matsayin wasu daga cikin hakkokin masu kamfanoni, wadanda wajibi ne a kiyaye su.

Jagoran ya ci gaba da cewa: To sai dai wajibi ne a dinga sanya ido kan kayayyakin da ake fita da su waje don tabbatar da kyaunsu, saboda idan har aka bari ana fita da kayayyaki marasa kyau, hakan zai bata sunan Iran da kuma cutar da abubuwan da ake fita da su waje.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada muhimmancin karfafa abubuwan da ake samarwa a cikin gida, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wajibi ne a kalli abubuwan da ake samarwa a cikin gida kallo na girmamawa, sannan kuma goyon bayan hakan a matsayin wani nauyi da ke wuya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar bai kamata a bari a dinga shigowa da kayayyakin kasashen waje wadanda ake samar da irin su a cikin gida ba, don haka sai ya ce: Wasu shagunan sun dora wa kansu nauyin cewa ba za a sayar da wani kaya wanda ba na cikin gida ba a wajen, wanda lalle hakan abin jinjinawa ne.

Jagoran ya nuna bacin ransa dangane da yadda ake samun wasu manyan shagunan wadanda wasunsu ma suna da alaka da gwamnati ma amma a samu cewa cike suke da kayayyakin waje, wanda hakan mummunan abu ne don kuwa yana haifar da rashin aiki ne a tsakanin ma'aikatan Iran da kuma ci gaba da karfafa ‘yan kasashen waje.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana fasa kwabrin kayayyaki a matsayin babban bala'in da ke cutar da kayayyakin da ake samarwa a cikin gida. Haka nan kuma yayin da yake kakkausar suka da rikon sakainar kashin da ake yi wa wannan lamarin ya bayyana cewar: Wajibi ne a sanya tsayayyen mutum a wannan bangaren, sannan kuma wajibi ne gwamnati ta karfafa cibiyar da abin shafa sannan kuma ta yi fada sosai da batun fasa kwabrin kayayyaki.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce abin nufi da fada masu fasa kwabrin kayayyaki shi ne irin manyan ‘yan kasuwa da suke shigowa da kwantenoni masu yawan gaske.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Isar da Iran zuwa ga kololuwar ci gaba irin na Musulunci ba wai take ne kawai ba, face dai wani abu ne da ya dogara da dalilai da kuma irin dama da karfin da ake da shi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Koda yake har ya zuwa yanzu makiya suna nan suna kokarin kafar ungulu, wanda babbar mai yin hakan ita ce kasar Amurka da yahudawan sahyoniya.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: A wasu lokuta Amurkawa suna korafin cewa me ya sa kuke mana irin wannan mummunan kallo? To akwai dalilan hakan, wanda kuma ba za mu iya rufe idanuwanmu mu ce ba mu gansu ba.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kafar ungulun da Amurka take yi a fagen ayyukan bankuna da musayen kudi a matsayin daya daga cikin dalilan da ya sanya Iran take mummunan kallo da rashin yarda da Amurka inda ya ce: To a halin yanzu dai hatta jami'an gwamnati suna magana kan irin kafar ungulun da Amurka take yi a fagen harkokin banki, amma me ya sa manyan bankunan duniya ba a shirye suke su yi mu'amala da Iran ba?

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Dalilin da ya sanya manyan bankunan duniya suka ki yin mu'amala da Iran, shi ne yanayin kyama da tsoron Iran da Amurka ta haifar sannan kuma take ci gaba da haifar da hakan.

Jagoran ya jaddada cewar: A lokuta da dama na sha fadin cewa Amurka ba abar yarda ba ce, a halin yanzu dai dalilin hakan yana ci gaba da bayyana.

Yayin da yake ishara da cewa a kan takarda Amurkawa sukan rubuta da kuma fadi da fatar baki cewa "Bankuna suna iya mu'amala da Iran", to amma a aikace suna ci gaba da haifar da yanayi na kiyayya da kyamar Iran, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Amurkawa suna fadin cewa Iran wata kasa ce mai goyon bayan ayyukan ta'addanci, sannan kuma mai yiyuwa ne a sanya mata takunkumi saboda wannan goyon bayan da take bai wa ta'addanci.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Shin wani sako irin wadannan maganganu suke isarwa ga bankuna da sauran bangarorin da suke son mu'amala da Iran? Sakon hakan shi ne cewa kada ku yi mu'amala da Iran. Don haka bankuna da masu zuba jari ‘yan kasashen waje za su ji tsoron yin hakan da Iran.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa: Koda yake dangane da batun ta'addanci, Amurkawa sun fi dukkanin ‘yan ta'adda muni. Bisa hujjoji da bayanan da ake da su, har ya zuwa yanzu suna ci gaba da taimakon ‘yan ta'adda.

Har ila yau Ayatullah Khamenei yayi ishara da wani salon da Amurka take amfani da shi wajen sanya tsoron Iran a cikin zukatan ‘yan kasashen da nufin hana su mu'amala ta banki da zuba jari da Iran inda ya ce: Suna ikirarin cewa yanayin cikin gidan Iran shi ne dalilin da ya sanya ‘yan kasashen waje ba sa son mu'amala da Iran, alhali kuwa a halin yanzu babu wata kasa a yankin nan da take da tsaron da Iran take da shi. Kai yanayin cikin gidan Iran, hatta ya dara irin yanayin cikin gidan Amurka, wadda a kullum a kan kashe wani adadi na mutane, kai hatta ma da na kasashen Turai wajen kyawun tsaro. Yanayin cikin gidan Iran, yanayi ne mai kyaun gaske duk kuwa da makiya ba sa son hakan.

Ayatullah Khamenei ya bayyana maganganun jami'an Amurka na cewa za su ci gaba da kiyaye tsari da yanayin takunkumin da aka sanya wa Iran a matsayin wani salon da Amurkawan suke amfani da shi wajen ci gaba da sanya tsoron mu'amala da Iran cikin zukatan bankuna da masu zuba jari ‘yan kasashen waje inda ya ce: Mu dai mu na fuskantar irin wannan makiyin ne. A saboda haka wajibi ne mu dinga la'akari da irin wannan makiyin a duk wani abin da muke son aikatawa.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu tsawon shekaru 37 din da suka gabata duk kuwa da kiyayyar Amurka, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Idan ma za su ci gaba da wannan kiyayyar har nan da shekaru dari masu zuwa ne, to kuwa haka din dai za mu ci gaba da samun ci gaba ko da kuwa ba sa so.

Jagoran ya kara da cewa: Amurka dai makiyarmu ce; shin mun kusace ta ne ko kuma ba mu kusace ba, shin mun fadi hakan ne ko kuma ba mu fadi ba. Wannan kiyayyar dai ba za ta kawo karshe ba.

Ayatullah Khamenei ya kirayi dukkanin jami'an bangarori uku na gwamnati da sauran cibiyoyi na juyin juya hali da kuma al'umma zuwa ga fahimtar irin karfi na cikin gida da ake da shi, inda ya ce: Lalle mu din nan tamkar Amirul Muminin (a.s) wadanda aka zalunta ne to amma muna da karfi. A saboda haka matukar muka yi amfani da irin karfin da muke da shi yadda ya dace, ko shakka babu za mu yi nasara a kan dukkanin matsalolin da aka haifar mana.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Ba ma cikin tsaka mai wuya kamar yadda kuma ba cikin sauki muke ba, don haka matukar muka dogara da irin karfin da muke da shi, ko shakka babu za mu kai ga nasarori masu yawa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya rufe jawabin nasa ne da ishara da zagaye na biyu na zaben ‘yan majalisar shawarar Musulunci da za a gudanar a Iran inda yayi Karin haske kan muhimmancin zaben da kuma kiran al'umma da su fito kwansu da kwarkwatarsu wajen kada kuri'arsu.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin dai sai da ministan aiki da jin dadin al'umma na Iran ya gabatar da jawabinsa da kuma irin ayyuan da ma'aikatar tasa ta aikata.

3492621

captcha