IQNA

Makaranci Dan Rwanda: Ina Kai sakon Muslunci Ga Mutanen Karkara

23:49 - May 15, 2016
Lambar Labari: 3480414
Bangaren kasa da kasa, wakilin kasar Rwanda a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ya bayyana cewa yana yin kokari domin zuwa kauyuka wajen isar da sakon mulsunci.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Iqna, Abdullah ma’ajur wakilin Rwanda agasar karatu da hardar kur’ani ta duniya da ke gudana karo na 33 a Iran, ya bayyana cewa akwai hanyoyi da yawa na isar da sakon muslunci ga mutanen nahiyarsa.

Ya ci gaba da cewa daya daga cikin hanyoyin da yake bi it ace zuwa kauyuka, domin yi ma mutanen karkara bayani kan addinin mslunci da kuma abin da yake kira zuwa gare shin a daga shiriya.

Kamar yadda bayyana cewa sakamakon hakan ya samu nasarar mulsuntar da wasu daga cikin mazauna karkara wadanda a da bas u san ma mene ne addinin mulsunci ba, domin kuwa babu wanda ya taba yi musu bayani a kansa.

Abdullah Ma’ajur ya ce ko shakka babu mutanen krklara sun fi saukin fahimtar bayani dangane da addinin muslunci, domin kuwa zukatansu a bude suke domin su karbi gaskiya a duk lokacin da ta zo musu.

Kasar Rwanda dai tana daga cikin kasashen Afirka, wadanda musulmia cikinsu marassa rinjaye ne, kuma gwamnatin kasar ba ta yin wani taimako ga cibiyoyin muslunci domin gudanar da ayyukansu.

Ya kara da cewa ayyukan da suke yi su ne da kansu suke hada kudadensu kuma ske gudanar da ayyukansu na isar da sakon muslunci ga al’umma, wadanda mafi yawansu mabiya addinin kirista ne.

3497698

captcha