IQNA

Radiyon Kur’ani Na Morocco Shi Ne Ya Fi yawan Masu saurare A Kasar

23:56 - May 18, 2016
Lambar Labari: 3480426
Bangaren kasa da kasa, wani sakamakon jin ra’ayin jama’a ya nuna cewa gidan radiyon kur’ani na kasar Morocco shi ne yafi kowane gidan radiyo a kasar yawan masu saurare a kasar.

Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CNN cewa, wannan jin ra’ayin jama’a ya nuna cewa kimanin mutane kasha 20 cikin dari na utanen kasar suna sauraren wannan gidan radio.

Wannan gidan radioyo ne yana hade ne da bababr tashar talabijin da radiyo mallakin gwamnatin kasar, kuma an zabe shi a matsayin gidan radiyo mafi yawan masu saurare na shekara.

Yayin da gidan radiyon kur’ani na garin Tanja ya samu kimanin kasha 12/24 cikin dari, wanda y aba shi damar zama na biyu, sai kuma Radio FM wanda shi kuma a tsakanin 5/12 cikin dari, wanda ya zo a matsayi na uku.

Jin ra’ayin jama’ar dai ya hada mutane 8538 ne na mutane daban-daban da aka ji ra’ayoyinsu, wadanda suka bayyana dalilansu wanda bisa hakan ne aka yi hukunci.

Abin tuni a nan dais hi ne, sarki Muhammad na shida shi ne wanda ya bude wannan gidan radiyo, domin bayar da dama ga makaranta kur’anu su rika gudanar da tilawa kamar yadda aka shirya, wanda kuma sannu a hankali a kara da wasu shirin na kur’ani wan da ya ja hankulan masu saurare.

3499209

captcha