
Kamfanin dullancin labaran Iqna ya nakalto daga Quds net cewa, wakilin palastinua majalisar dinkin duniya a cikin wata wasika da aike wa Ban Ki Moon tare da goyon bayan wakilai na dukkanin kasashen musulmi da na larabawa 57, ya bukaci da a kawar da bajen kiln Isra’ila daga cikin ginin mjalisar dinkin duniya.
A cikin wasikar an bayyana cewa ana bukatar a janye wadandannan kayayyakin da Isra’ila ta baje a cikin ginin wannan majalisa tare da amincewar wadannan kasashe, wanda kuma hakan babban lamari ne ga haramtacciyar kasar yahudawan.
A wannan baje kolin Isra’ila ta nuna hotuna na yawo da hankulan mutane, da suka hada da na masallacin Quds, da kuma yadda palastinawa ske rayuwa tare da yahdawa kowa na hidimarsa, gami da wasu daga cikin wurare masu tsarki na muslmi da larabawa na tarihi da ke wurin.
Babbar manufar haramtacciyar gwamnatin yahudawan dai it ace dauke hankulan al’ummomin duniya daga irin tabargazar da take tafkawa na kisan gilla da cin zalun da take yi dare da rana akan al’ummar palastinu.
Wakilin al’ummar palastinu a majalisar dinkin duniya dai ya bayyana hakana matsayin wani cin zarafi ga al’ummar palastinawa da kuma larabawa da musulmi.
An kafa wannan baje koli ne a wani wuri da ke da cunkoson jama’a acikin ginin majalisar dinkin duniya domin hakan ya ja hankulan mutane.