
Kamfanin dillanicn labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, wasu daga cikin masana a kasar Masar sun soki yadda wannan hoto ya nuna ganawar.
Wani daya daga cikin masana a bangaren sadarwa a kasar Ahmad Al-shahawi shi ne ya fitar da wanna hoto a cikin shafinsa na yanar gizo na sada zumunta wato facebook,inda y ace hakika hankalinsa ya kasa kama abin da ya gani, domin kuwa ko shakka babu Ahmad Tayyib yana wakiltar babbar cibiyar muslunci ta duniya ne a lokacin ganawarsa da paparoma, yayin da shi kuma yake wakiltar babbar darikar mabiya addinin kiristanci, saboda haka ya kama a ce akwai daidaito a tsakaninsu ko da ta fuskar zama, amma sai ga malamin ya zauna kamar malami da almajirissa.
Mahmd Alqaud shi ma malami ne a bangaren adabi ya ce hakan yay i hannun riga da al’adun mutanen Masar.
Ganawar sheikhul Azhar da paparoma ta jawo batutuwa da dama, da hakan ya hada batn cewa shin wannan ziyara ta kebance shi ne shi kadai ko kuwa yana wakiltar musulmi ne baki daya, domin kuwa akwai batutuwa da ya kamata ya bijiro da su da suka hada har batun Julia Rajini wani dalibi musulmi da shekaru 28 da aka kasha a kasar wanda aka yi shiru a kansa.
Haka annkuma a lokacinda yake ziyarar yan ta’adda sun kaddamar da hare-hare a cikin kasashen musulmi amma bai ce komai kan hakan ba, musamman kisan da suke yi kan mutanen Falluja, wanda hakan ya saya alamar tambaya kan cewa batu da yake na nemn hadin kan musulmi akwai bangarancia cikinsa.