IQNA

Ba A Cimma Matsaya Guda Kan Batun Aikin Hajji Tsakanin Iran Da Saudiyya ba

23:47 - May 27, 2016
Lambar Labari: 3480454
Bangaren kasa da kasa, har yanzu ba a cimma matsaya guda daya ta karshe ba kan batun aiki hajji tsakanin Iran da kuma mahukuntan kasar Saudiyya ba.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na Shafaqana cewa ya nakalto daga jaridar Sharq Alausat cewa, tawqagar Iran karkashin jagorancin Said Wahidi ba su cimma matsaya guda daya ta karshe ba kan batun aiki hajji tsakanin Iran da kuma mahukuntan kasar Saudiyya ba saboda rashin tawagar Iran a tattaunawar da aka shirya.

Jaridar ta ce an ajiye Magana kan cewa za a gudanar da wannan zama a Jidda a tsakanin bangarorin biyu, amma tawagar Iran ba ta halarta ba, kuma ba aji dalilinsu na yin hakan ba.

Sharq Alausat ta ce hukumar kula da ayyukan hajji da umrah ta Saudiyya tan ada masaniya kan tafiyar da tawagar Iran ta yi zuwa Makka, amma an ajiye kan cewa da sun dawo a nan take a gudanar da zama a domin kamala maganar, sai hakan bai kasance ba.

3501390

captcha