IQNA

Shekhul Azhar Gwarzon Shekara Na gasar Dubai

23:36 - June 01, 2016
Lambar Labari: 3480468
Bangaren kasa da kasa, cibiyar da ke shirya gasar kuur’ani ta kasa da kasa a Dubai ta zabi Ahamad tayyib babban malamin Azahar a matsayin gwarzon shekara.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «egynews.net» cewa, Ibrahim Bu Malha wanda shi ne abbabn darakta mai kula da shirya wannan gasa ya bayyana cewa, sun zabi Ahmad Tayyib ne a matsayin gwarzon shekara, saboda irin rawar da yake takawa ta fuskar isar da sakon addini zuwa ga kasashen duniya.

Ya ce sheikhul Azahar ya yi rubuce-rubuce da dama a bangarori daban-daban na addinin muslunci, wadanda sun cancanci yabo da girmamawa a gasar kur’ani ta Dubai a ranar 20 ga watan Ramadan na bana.

Ibrahim Bu Malha ya ce baya ga koyarwa a wannan babbar jami’a ta musulunci, a halin yanzu kuma shi ne bababn mufti mai bayar da fatawa a wanann cibiya.

Abin tuni a nan dais hi ne, tun daga shekara ta 1997 an bayar da kyautuka na gasar Dubai ga mutane da dama wadanda ska yi rubutu a bangarori na addinin muslunci a duniya.

Gasar kur’ani ta Dubai za ta fara ne tun daga ranar 10 ga watan Ramadan mai kamawa.

3502935

captcha