IQNA

An Daure Wani Mutum Da Ya Ci Zarafin Wata 'Yar Majalisa Musulma A Belgium

19:18 - June 02, 2016
Lambar Labari: 3480471
Bangaren kasa da kasa, Kotu ta yanke hukuncin daurin watanni 6 a gidan kaso a kan wani mutum da ya ci zarafin wata 'yar majalisar dokokin kasar Belgium musulma saboda addininta.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Jaridar Yani Shafaq ta kasar Turkiya ta bayar da rahoton cewa, matar mai suna Mahinur Ozdemir, wadda ita ce mace musulma ta farko da ta fara zama 'yar majalisar dokoki a kasar Belgium, ta fuskanci cin zarafi da batanci daga wani mutum ta hanyar kafar sadarwa ta yanar gizo.

Mahinur Ozdemir ba ta yi wata--wata ba sai ta maka shi kotu, inda aka gano shi kuma aka gurfanar da shi, daga karshe dai kotu ta yanke hukuncin daurin watanni 6 a gidan kaso a kansa, saboda cin zarafin wannan musulma da ya yi saboda addininta.

Matar ta ce ta yi farin cikin ganin wanann kotu ta yanke irin wannan hukunci, domin ya zama darasi ga duk wani wanda yake tunani yin izgili ko batanci ga wata musulma a kasar saboda akidarta ta musulunci.

Ta ce tana kira ga masu mu'amala da hanyoyin sadarwa na yanar gizo da su yi amfani da hakan ta hanyoyi da suka dace, maimako cin zarafi da batunci ga wasu, musamman ma idan lamari ya shafi addini ko akida, domin kowa yana girmama abin da ya yi imani da shi.

3503206

captcha