Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa
ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na tashar talabijin ta Alalam ta
bayar da rahoton cewa, Yahuda Glik wanda malamin yahudawa ne mai matsayin
khakham, kuma dan majalisar Isra'ila ta Knesset, ya yi barazanar cewa, zai
jagoranci yahudawa domin rusa masallacin Quds, matukar dai cibiyar palastinawa
mai kula da harkokin addinin muslunci a birnin Quds ta ci gaba da biris da
kiran da suka yi mata, na ta amince a raba masallacin Quds biyu, daya bangaren
na musulmi, daya bangaren kuma na yahudawa.
Wannan furuci dai yana ci gaba da fuskantar kakkausar suka daga bangarori daban-daban na musulmi, kamar yadda a nasa bangaren babban malami mai bayar da fatawa a birnin Quds Sheikh Ikrama Sabri ya yi Allawadai da wannan furuci da ya fito daga bakin daya daga cikin malaman yahudawa kuma dan siyasa, inda ya ce wannan furuci ne mai matukar hadari, wanda al'ummar palastinu da sauran musulmin duniya ba za su taba amincewa da shi ba.
Sheikh Ikrama ya kara da cewa, duk abin da yake faruwa da sanin gwamnatin Isra'ila ne, domin kuwa ita ce take bayar da kariya ga yahudawa masu tsatsauran ra'ayi da suke cin zarafin musulmi da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki na addinin musulunci, da hakan ya hada har da masallacin Quds mai alfarma, kuma alkiblar musulmi ta farko.