IQNA

Gasar Kur’ani Mai Tsarki Ta Mabiya Mazhabar Shi’a A Bahrain

23:08 - June 05, 2016
Lambar Labari: 3480480
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta Furqan wadda ta kebanci mabiya mzhabar shi’a a kasar Bahrain.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Qaf cewa, za a gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta Furqan wadda ta kebanci mabiya mazhabar shi’a a kasar Bahrain mai taken Furqan, tare da hadin gwiwa da cibiyar Ahalul bait (AS) ta kasar Kuwait.

Gsar dai za ta kunshi bangarori biyu ne na matasa wadanda suke daga shekaru 15 abin da ya yi sama wato wadanda aka Haifa daga shekarar 2002 abin ya yi kasa za su karanta tafsri da rdar surat Mursalat.

Wadanda suke kasa da shekaru 15 kuma wato da aka Haifa daga shekara ta 2001 abin ya yi sama, za su karanta Naml da kuma tafsirinta.

Wannan ciobiya mai kula da ayyukan kur’ani ta kasar Bahrain ta mabiya mazhabar shi’a za ta kamala rijistar sunaye ne a cikin mako mai zuwa.

3503788

captcha