IQNA

Cibiyar Fatawa Ta Ce Ramadan Dama Ce Wajen Yaki Da Kyamar Muslunci

20:17 - June 09, 2016
Lambar Labari: 3480497
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar bayar da fatawa a kasar ta yi kira ga musulmi musamman wadanda ke zaune a turai su yi amfani da wannan dama ta Ramadan domin isar da sakon muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na egynews.net cewa, babbar cibiyar bayar da fatawa a kasar ta yi kira ga musulmi musamman wadanda ke zaune a turai su yi amfani da wannan dama ta Ramadan domin isar da sakon muslunci da kuma yakar akidar nan ta kyamar wannan addinin.

Bayanin y ace musulmi a duk inda sukea cikin kasashen duniya musaman ma a kasashen da ban a musuli ba za su iya shirya tarukan buda baki tare da gayyatar musulmi da wadanda ba musumi zuwa buda bakin.

Haka nan kuma sais u yi amfani da wanna damar domin yin tunatarwa da kuma amsa tambayoyi daga wadanda ske bukatar sanin koyarwar musulunci, maimakon barin mutane suna kallon musulmi da wata mahanga ta daban wanda hakan ke saka musulmi cikin mawuyacin hali a cikin irin wadannan kasashe.

Ya kara da cewa mafi yawan halaye na tsangwama da ake nuna ma musulmi hakan na faruwa sakamakon rashin sanin hakikanin menen addinin muslunci, domin kwa wadanda suke aiwatar da ta’addanci da sunan muslunci sun bata sunan wanann addini.

Haka nan kuma cibiyar ta ce za a iya shirya taruka da suka kebanci musulmi musamamn domin kara wayar da kansu, da kuma nisanta da akidar tsatsauran ra’ayin, da mummunar fahimta kan addini, wadda kan matasa zuwa shiga kungiyoyin ta’addanci, sna zaton cewa musulunci suke yi.

3504881

captcha