IQNA

Za Bayar Da Hotu A Ranakun Idin Muslunci A Filadelfia

20:22 - June 09, 2016
Lambar Labari: 3480499
Bangaren kasa da kasa, magajin garin birnin Filadelfia a kasar Amurka ya sanar da cewa za a rika bayar da hutu a makarantun firamare da sakandare a ranakun hutun nmusuluci.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The Daily Pennsylvanian cewa, majalisar dokokin jahar za ta amince da wani dafkarun kudri, wanda zai bayar da damar a rika yin hutua makarantu a cikin shekaru 2016 da 2017 a ranakun hutun muslunci.

Babban daraktan harkokin ilimi na birnin Filadelfia ya bayyana cwa hakika suna alfahari da cewa jaharsu ta fara aiwatar da wanann lamari, domin kuwa hakan ya kara tabbatar da kyakyawar dangataka da ke tsakanin dukkanin al'ummomin jahar.

Tun a cikin shekara ta 2005 ce dai aka mika wannan bukata ga majalisar jahar, wadda kuma ake sa ran daga wanann shekara za ta fara aiki a hukumance.

Kimanin dalibai 200,000 ne musulmi suke karatua makarantun birnin Filadelfia, wanda hakan ke nufin cewa kashi 20 cikin dari na dalin birnin mabiya addinin muslunci ne.

3505422
captcha