
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashr Press TV cewa, an gudanar da janazar fitaccen dan was an dambe na duniya Muhammad Ali mahaifarsa da ke Lui wel afilin wasa na KFC youm center a tsakiyar dubban magoya bayansa.
Janazar dai ta samu halartar fitattun yan wasa na duniya da kuma fitattun mutane daga sassa daban-daban na duniya.
Muhammad Ali ai ya rasu ne yana da shekaru 74 da haihuwa a duniya., a wani asibiti da ke garin Arizona sakamakon fama da matsalar karancin lumfashi, haka nan kuma yay i fama da matsalar ciwon jijjiga.