Mahdi Gholam Najad a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna
ya bayyana cewa, ya kammala shirinsa domin shiga wannan gasa, duk kuwa da cewa
kwai babban kalu bale a gabansa, wanda yake bukatar ya maida hankali kansa
matuka.
Ya ce a yau zai kara da makaranta daga kasashen najeriya, Azarbaijan, Mali da kuma Kossovo, inda kowannensu ke bukatar ya samu makin da ake bukata a wannan mataki.
Haka nan kuma ya yi ishara da cewa a wannan gasa an gayyaci makaranta da mahardata, wadanda ga alama suna da karfi sosai, wanda wasu daga cikinsu sun fi makarantan Iran gogewa wajen halartar gasa a wasu kasashen na duniya.
Wannan gasa dai za a gudanar da ita ne a babban masallacin Fateh da ke birnin Istanbul na kasar, wanda kuma shi ne karo na hudu a jere da ake gudanar da wannan gasa a kowace shekara.
Daga karshe y ace yana barar addu'a daga dukkanin mutanen kasar domin samun nasara a wannan gasa, domin ya gudanar da it aba tare da wata matsala ba, musamman ma ganin cewa wannan tana daya daga cikin irin da da ke samun wakilcin mutum daya kawai daga kasar.