
Mahdi Gholamnejad a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayyana cewa, ya gabatar da karantun nasa a ne a masallacin Alfateh da ke Istanbul, bayan da ya samu gayyata daga masu kula da masallacin.
Ya ce ya yi karatun kur’ani mai tsarki daga aya ta 285 zuwa ta 286 a cikin surat Baqarah, tare da halartar wasu daga manyan malamai na addini na kasar Turkiya a masallacin.
Tun a shekaran jiya ne aka aike da goron gayyata gare shi domin gudanar da wannan karatu a cikin wannan masallaci, amma saboda karancin lokaci, hakan bai samu ba.
Wannan makaranci dai ya halarci gasar kur’ani ta kasa da kasa da ake gudanarwa a kasar Turkiya ta wannan shekara, wadda kuma za a kammalata a kwanaki biyu masu, inda za a sanar da sunayen wadanda suka nuna kwazo a gasar, tare da ba su kyautuka.