
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, Barack Obama ya mayar wa Trump da martani kan cewa, abin da ya faru na kai hari a Orlando ba dalili ba ne na kiran dukkanin musulmi 'yan ta'adda, ko kuma yin kira da a hana musulmi shiga Amurka kamar yadda Donald Trump ke yin kira.
Obama ya ce addinin musulunci ba addinin ta'addanci ba ne, kuma 'yan ta'adda ba suna wakiltar sauran musulmi ba ne, a kan haka dora alhakin abin da wasu 'yan ta'adda ke yi a kan dukkanin musulmi ba adalci ba ne, kuma Amurka kasa ce da tsarinta ke girma a akida da addini kowa.
Trump ya zafafa kiransa na hama musulmi shiga Amurka idan an zabe shi a matsayin shugaban Amurka
Donal Trump dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar Republican a kasar Amurka ya kara karfafa shirinsa na hana musulmi shiga Amurka bayan harin da aka kai a wani gidan shaye shaye a jihar Florida idan an zabe shi.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa Trump ya dauki wannan harin a matsayin wata dama na sukar abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton.
A nata bangaren Hillari Clinton na jam'iyyar Democrate ta yi All..wadai da hariin ta kuma bukaci ya yi bincike a dauki matakan da suka dace ba tare da an cutar da musulmi tsiraru a kasar ba.
Donal Trumps dai ya ce idan an zabe shi zai hana shigowar musulmi yan gudun hijira daga kasashen musulmi zuwa kasar Amurka don kada su lalata 'ya'yansu da mummunan akidu .