IQNA

Cibiyar Yada Al’adun Muslunci Ta Yi Allawadai Da Cin zarafin Sheikh Isa Kasim

23:29 - June 22, 2016
Lambar Labari: 3480538
Bangaren kasa da kasa, cibiyar yada al’adun muslunci ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da janye izin zama dan kasa daga kan Ayatollah Isa Kasim a Bahrain.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, cibiyar ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da janye izin zama dan kasa a kan Ayatollah Isa Kasim da mahukuntan masarautar mulkin mulukiya ta Bahrain ta yi.

A daya bangaren malaman addini da manyan manyan 'yan siyasan a kasashen musulmi na ci gaba da Allah wadai da gwamnatin kasar Bahrain saboda soke takardun shaidar zama dan kasa da ta yi wa babban malamin Shi'a na kasar Ayatullah Sheikh Isa Qasim.

A jamhuriyar muslunci manyan malamai da maraja'an Shi'a da suke biranan kasar sun yi kakkausar suka ga gwamnatin kasar Bahrain din saboda wannan mataki da ta dauka na soke takardun shaidar zama dan kasa na Sheik Isa Qasim suna masu jan kunnen gwamnatin da su guji abin da zai biyo baya.

A cikin wani sako da ya fitar malam Safi daya daga cikin manyan maraja'an duniyar Shia da ke birnin Qum ya bayyana cewar wajibi ne malaman Musulunci su fito su yi Allah wadai da wannan danyen aikin. Shi ma a nasa bangaren malaman makarim daya daga cikin maraja'an duniyar Shi'an ya ce gwamnatin Bahrain ta kama hanyar faduwa kasa warwas sakamakon wannan aiki na ta.

Malaman addini da kungiyoyi daban-daban a kasashen duniya ma sun yi Allah wadai da wannan danyen aikin na gwamnatin Bahrain.

Har ya zuwa yanzu dai al'ummar kasar Bahrain din suna ci gaba da zanga-zangogi don nuna rashin amincewarsu da wannan hukunci na gwamnatin, suna masu jan kunnen mahukuntan da cewa taba lafiyar Sheik Qasim wani abu ne ba za su taba amincewa da shi ba.

A kwanakin baya ne ma'aikatar cikin gida ta kasar ta Bahrain ta sanar da soke takardar zama dan kasar na Sheikh Qassim.

3509638

captcha