IQNA

Muhammad Rasul Takbiri Zai Wakilci Iran A Gasar Kur’ani Ta Algeriya

23:31 - June 22, 2016
Lambar Labari: 3480539
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Rasul Takbiri shi ne zai wakilci jamhuriyar musulunci ta Iran a gasar karatun kur’ani ta duniya a kasar Algeriya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, gasar kur’ani ta Algeriya za a gudanar da ita ne nan da yan kwanaki masu zuwa daga 20 zuwa 26 ga watan Ramadan mai alfarma.

An haifi Muhammad Rasul Takbiri a birnin Tehran, kuma ya kasance yana da tsari na musamman wajen hardar kur’ani mai tsarki.

A shekarar da ta gabata ce dai ya karbi takardun shedar kamala hardar kur’ani mai tsarki, kuma takardunsa sun nunaa cewa hardarsa tana da kyau matuka.

Haka nan kuma a shekarar da ta gabata Muhammad Khakpour wanda ya zo na biyu a gasar kur’ani ta kasa baki shi ne ya wakilci Iran a gasar kur’ani ta kasar Algeriya.

Ali Reza Faizi da Paiman Ayazi, su ne suka wakilci Iran a gasar duniya ta kasar Algeriya a cikin shekarun 2013 da kuma 2014, inda suka samu matsayi na hudu a gasar baki daya.

3509518

captcha