IQNA

Jami'an 'Yan Sandan Gwamnatin Saudiyya Sun harbe Wani Farar Hula A yankin Awamiyyah

23:42 - June 23, 2016
Lambar Labari: 3480542
Bangaren kasa da kasa, Jami'an 'yan sanda na kasar Saudiyya sun harbe wani farar hula har lahira a garin Al-awamiyyah da ke gabacin kasar ba tare da bayyana wani dalili na yin hakan ba.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga tashar talabijin ta Press TV ta bayar da rahoton cewa, jami'an 'yan sandan sun kaddamar da farmakin ne a kan gidan Abdulrahim Ali Alfaraj, bisa zarginsa da cewa ya jefi jami'an tsaro, bayan kashe shi har lahira bisa wannan zargi a yammacin jiya Laraba, jami'an 'yan sanda na masarautar mulkin mulukiyya ta Al Saud sun rusa gidan baki daya.

Tun a cikin watan Fabrairun shekara ta 2011 ce dai alummar yankunan gabashin kasar saudiyya wadanda mabiya mazhabar shi'a ne, suka fara yunkurin ganin an ba su hakkokinsu da ake danne musu a matsayinsu na 'yan kasa, wadanda suke korafin cewa dukkanin arzikin kasar na man fetur da iskar gas da tattailin arzikin kasar ya dogara akansa, daga yankinsu ake fitar da shi, amma suna rayuwa a cikin yunwa da talauci da rashin ayyukan yi.

Wannan dai shi ne babban dalilin da ya sanya mahukun kasar Saudiyya suka kame Sheik Bakir Nimr suka kashe, saboda nuna goyon bayansa ga masu fafutukar neman hakkokin al'ummomin yankunan gabashin kasar.

3509785

captcha