
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Mir’at Bahrain cewa, mahukuntan Bahrain sun kmae wasu manyan malamai guda 6 na kasar bisa tuhumarsu da cewa suna mara baya ga Ayatollah Isa Qasim.
Wadannan malamai 6 su ne Mahmud Alali, Hamza Diri, Fadel Zaki, Munir Ma’atuk, Ibrahim Safa, Ali Rahma, wadanmda aka kira su da sunan bincike a kansu.
Cibiyoyin kasa da kasa sun biyo sauran sahun kungiyoyi da al'ummomin duniya wajen yin Allah wadai da nuna damuwarsu kan siyasar tursasawa da amfani da karfi na gwamnatin kasar Bahrain musamman bayan soke takardar shaidar dan kasa na babban malamin Shi'a na kasar Ayatullah Sheik Isa Qasim da gwamnatin ta yi.
A nata bangaren, Majalisar Dinkin Duniya ta bakin babban mai ba da shawara kan hanyoyin hana kisan kare dangi na dieng, ta bayyana matakin da gwamnatin Bahrain din ta dauka na soke takardar dan kasar Sheik Isa Qasim a matsayin abu mai muni kuma abin Allah wadai inda ya kirayi gwamnatin Al-Khalifa din da ta mutumta hakkin da al'ummar kasar suke da shi na gudanar da gangami nuna rashin amincewarsu kan siyasar gwamnatin kasar cikin ruwan sanyi da kuma girmama dokokin kasa da kasa na bangaren kare hakkokin bil'adama.
Jami'in ya kara da cewa amfani da karfi koda wasa ba zai kawo karshen nuna rashin amincewar da al'ummar Bahrain suke yi, face ma dai zai iya kara kaimi da kuma zafin hakan ne.
Har ila yau ta bayyana soke takardar dan kasar Sheikh Qasim da gwamnatin Bahrain din ta yi a matsayin wani abin da ba za a iya amincewa da shi ba. Yayin da take bayyana hakan mai magana da yawun ofishin kare hakkokin bil'adama na MDD, Ravina Shamsadani ta ce bisa la'akari da cewa ba a gurfanar da Sheik Isa Qasim a gaban wata kotu ba, don haka babu yadda za a iya amincewa da hakan saboda abu ne da bai dace ba.
Ita ma a nata bangaren kungiyar kare hakkokin bil'adaman ta Human Rights Watch, cikin wata sanarwa da ta fitar, ta yi kakkausar suka ga halin ko in kula da kasashen yammaci suke nunawa dangane da danyen aikin da gwamnatin Bahrain din take aikatawa, kamar yadda kuma ta kirayi gwamnatin Bahrain din da ta yi soke wannan matsaya da ta dauka kan Sheik Isa Qasim sannan kuma ta sako masu rajin kare hakkokin bil'adama da take tsare da su.
Kungiyar Humar Rights Watch din ta ci gaba da cewa har ya zuwa yanzu babu wata kwakkwarar shaida da gwamnatin Bahrain din ta gabatar dangane da zargin da take yi wa Shiek Isa Qasim da kuma jam'iyyar Al-Wifaq ta 'yan adawar kasar da ta haramta.
Baya ga wadannan kungiyoyin wasu 'yan majalisar kungiyar Tarayyar Turai ma sun yi Allah wadai da wannan matsaya da gwamnatin Bahrain din ta dauka suna masu bayyana hakan a matsayin zalunci. Yayin da take magana kan hakan, shugabar jam'iyyar rebecca harms ta bayyana matakin da cewa zalunci ne wanda kuma zai kara dagula lamurra ne a Bahrain.
Ko shakka babu ci gaba da yin Allah wadai da bakar siyasar gwamnatin gidan sarautar Al-Khalifa na kasar Bahrain na amfani da karfi a kan al'ummar kasar da cibiyoyin kasa da kasa da kuma manyan 'yan siyasa na duniya suke yi wani lamari ne da ke nuni da irin munin da wannan zaluncin yayi ne da kuma cewa al'ummomin duniya fa sun fara kosawa da gwamnatin ta Bahrain wanda daga karshe dai ba ta da wata mafita face amsa bukatun al'ummar kasar masu neman 'yanci da hakkokinsu cikin ruwan sanyi ba tare da amfani da karfi ba.