IQNA

Fara Gasar Kur'ani ta Kasar Mauritania

23:49 - June 25, 2016
Lambar Labari: 3480550
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta kasa a Mauritania tare da halartar makaranta da mahardata daga sassan kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saharamedias cewa, an fara gudanar da wannan gasa ne tare da hadin gwaiwa tsakanin babbar cibiyar muslunci ta kasar da kuam cibiyar shirya gasar kur'ania garin Nawazibu.

Bayanin y ace wannan gasa ta hada yara matasa maza da mata, kamar yadda kuma za ta kunshi bangarpri daban-daban na harda da kuma karatu.

Yara da shekarunsu suka kama da 10 zuwa 20 za su yi harda a juzui natalatin zuwa sama, sai kuma daga shekara 10 zuwa 18 za su yi kasa da kasa da haka, sai kuma shekaru 9 zuwa 14 za su yi harda daga juzu sha biyar zuwa kasa, yan mata daga shekaru 8 zuwa 14 za su yi hardar juzui bakawai, sai kuma yan mata da yan maza daga shekaru 5 zuwa 8 za su yi juzui kasa da biyar.

Ahmad Wuld Hadi shi ne shugaban bangaren kula da harkokin addini na yankin Nawazibu birni na biyu mafi girma a kasar, ya bayyana cewa babbar manufar gudanar da wannan gasa ta matasa ita ce karfafa gwiwarsu a kan harkokin da suka shafi kur'ani mai tsarki, domin hakan ya yi tasiri gare su tun daga kuruciya.

Daga karshe ya yi fatan cewa iyaye za su mayar da hankali wajen mara baya ga cibiyoyin da suke shirya gudanar da irin wannan gasa a fadin kasar, domin tura yaransu su koyi kur'ani wanda shi ne hanyar tsira.

3510111
captcha