Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta
cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na Ina cewa, A cikin bayanin da
kungiyar ta fitar, ta bukaci gwamnatin kasar Myanmar da ta gaggauta gudanar da
bicike kan wannan lamari, tare da kame dukkanin wadanda suke da hannu da kuma
gurfanar da su a gaban kuliya.
Bayanin ya ce abin da musulmi suke fuskanta na cin zarafi da kisa da tsangwama a kasar Myanmar ya wuce iyaka, kuma hakki a kan gwamnatin kasar ta dauki matakin kare rayukan mabiya addinin muslunci a kasar, domin rashin yin hakan zai sanya alamar tambaya a kan matsayin gwamnatin kasar dangane da abin da ake yi ma muuslmi.
A daren Alhamis da ta gabata ce dai wasu masu bin addinin buda da yawansu ya kai kimanin 200 suka kai farmaki kan wani masallaci a yankin Bago na kasar ta Myyanmar, inda suka banka ma masallacin wuta tare da kone shi kurmus, musulmin da ke wurin sun tsere zuwa wani ofishin 'yan sanda da ke kusa domin samun kariya.
Mabiya addinin muslunci 'yan kabilar Rohingya da suke zaune akasar Myyanmar suna fuskantar matsaloli na kyama da cin zarafi da kisa daga masu tsatsauran raayin addinin Buda, wadanda suke kallon musulmin a matsayin baki haure, kuma dole su bar kasar.