
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misr 24 cewa, a jiya ne aka fara gudanar da gasar kur’ani mai ta kasa da kasa a birnin Algiers na kasar Aljeriya karo na 13 tare da harlartar wakilai daga kasashe 56 na duniya wanda zai hada bangarori na hardada tajwidi.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan gasa ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar ce ta dauki nauyin shiryata.
Haka nan kuma akwai kyautuka da za a bayar ga wadanda suka nuna kwazo na dinari miliyan daya ga wanda ya zo na daya a bangaren tafsiri, sai kuma dubu 800 ga wanda ya zo na biyu, yayin da na uku zai samu dubu 500.
Dukkanin wadanda suke halartar gasar dai suna kasa da shekaru 25 ne.
A bangaren harda kuwa wadda ta kebanci kananan yara, za a bayar da kyautuka ga na daya da na biyu da na uku kamar haka, dubu 500 sa kuma dubu 300, da kuma dubu 200.
Gasar dai wadda aka fara gudanarwa a jiya, baya ga makaranta maza akwai mata 8 daga cikinsu.
Ministan harkokin addini na kasar Aljeriya Aiman Suwaid ya bayyana cewa, babban alkalin da zai jagoranci alkalancin gasar dai dan kasar Syria ne.
Muhammad Rasul Takbiri daga kasar Iran shi ne yake wakiltar kasar a wannan gasa, wanda ya kasance a sahun gaba daga cikin wadanda suka lashe gasar kasa baki daya a Iran, inda ya zo a mataki na biyu.