
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoto daga kasar ta Aljeriya cewa,a gobe ne bayan sallar magariba za a kamala taron gasar a babban masallacin Algiers tare da sanar da sunayen mutanen da suka nuna kwazoa gasar.
Bisa ga wannan rahoto, wakilin Iran a wanann gasar Muhammad Rasul Takbiri yana daga cikin wadanda suka nuna kwazo matuka, inda ya gudanar da karatunsa na karshe ba tare da an ci shi gyara ko guda daya ba, Sayyd Mahdi malamin kur’ani daga Iran ne yake y masa rakiya.
Wannan gasa dai wadda tana daya daga cikin manya irinta na duniya da ake gudanarwa akasar ta Aljeriya tana samun halartar wakilai daga kasashen duniya 56, da suka hada da na larabawa da kuma na musulmi da ma wadanda ban a musulmi ba.
Rahoton ya kara da cewa kyautuka da za a bayar ga wadanda suka nuna kwazo na dinari miliyan daya ga wanda ya zo na daya a bangaren tafsiri, sai kuma dubu 800 ga wanda ya zo na biyu, yayin da na uku zai samu dubu 500.