
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tunis.icro cewa, gasar ta gudana baki daya a cikin nasara.
Muhammad Asadi Muwahhad shi ne shugaba ofishin yada al’adu na kasar Iran a kasar Tunisia, shi ne kuma ya jagoranci mika kyautuka ga mutane 10 wadanda suka fi nuna kwazo a gasar.
An gabatar da jawabai a taron rufe wannan gasa, wadanda suka mayar da hankali ga muhimanci yin aiki da koyar kur’ani a tsakanin matasa, tare da kauce ma gurbatacciyar fahimta da ake yada dangane kur’ani da koyarwarsa.
Asadi Muwahhadi a lokacin da yake gabatar da nasa jawabin ya yi ishara da hadisin manzon Allah (SAW) da ke cewa, idan lamurran sun rikice muku kamar dare mai tsananin duhu, to na hore ku da komawa ga kur’ani.
Inda ya ce ko shakka babu babbar mafita ga musulmi it ace yin riko da hakikanin koyarwar kur’ani kamar yadda manzo ya koyar da musulmi hakan shi ne mafita.
Daga karshe an bayar da wasu kyautuka na musamman ga dukkanin mahalarta wurin, da ska hada har da kweafin kur’ani bugun kasar Iran.