IQNA

'Yan Ta'adan Daesh Sun Hana Jamaa Ziyartar Kabrukan Danginsu A Ranar Sallah

23:36 - July 07, 2016
Lambar Labari: 3480589
Bangaren kasa dakasa, 'yan sandan 'yan ta'addan ISIS sun hana jama'a a garin Mausil na kasar Iraki ziyartar kabrukan danginsu a ranar idin karamar sallah domin yi musu addu'a.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bratha cewa, 'yan ta'addan sun dauki kwarar matakai na hana al'umma zuwa wannan ziyara wadda suka saba yi tsawon daruruwan shekarau.

'yan ta'addan da ake kira 'yan sanda, suna yin amfani da karfi wajen kora da tarwatsa jama'a aduk lokacin da suka fahimci cewa za su ziyarci kabrukan danginsu ne kamar yadda aka sabayi a wannan gari.

Inda suke ce musu yin hakan kafirci ne da kuma shirka, saboda haka daular muslunci ta hana yin haka, kuma duk wada ya nace a kan cewa zai ziyarci wani kabari daga cikin kabrukan danginsa, to hukuncin yin shirka da kafirci zai hau kansa.

Tun a cikin shekara ta 2014 da ta gabata ce tare da taimakon wasu kasashen larabawa masu makwabtaka da kasar, yan ta'addan suka kwace iko da birnin Mausil, inda suka yi mutane kimanin dubu daya da dari bakwai kisan gilla a rana guda, bias hujjar cewa su yan shi'a ne.

3513396

captcha