IQNA

Kungiyar Hamas Da Sauran Kungiyoyin Palastinawa Sun Mayar Wa Saudiyya Da Martani

22:07 - July 11, 2016
1
Lambar Labari: 3480599
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar Hamas tare da sauran kungiyoyin palastinawa sun mayarwa Saudiyya da martani dangane da siffanta su da 'yan ta'adda da tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar ya yi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafin watsa labarai na yanar gizo mallakin kungiyar Hamas ya bayar da sanarwar cewa, kalaman da suka fito daga bakin Turki Faisal tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar Saudiyya a gaban taron kungiyar MKO a birnin Paris kan kungiyoyin Palastinawa da ke yaki da zalunci da mamayar Isra'ila babban abin kunya ne.

Bayanin ya ce kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin gwagwarmaya dukkaninsu kungiyoyi ne na palastinawa zalla da suke gwagwarmaya domin kare martabar al'ummar musulmi ta Palastinu da wurare masu tsarki da ke fuskantar tozrci da daga yahudawan sahyuniya, amma bayyana su a matsayin 'yan ta'adda masu yi ma wasu aiki da yarima Turki Faisal ya yi, hakan yana matsayin wata babbar hidima ga Isra'ila, kuma hakan takar an bayar da lasisi ne ga Israila kan ta ci gaba da ta'addancinta kan al'ummar Palastinu.

Ita ma a nata a nata bangaren kungiyar Jihadul Islami ta bayyana kalaman na yarima Turki Faisal da cewa alama ce ta kaskanci da wulakanta kai a gaban yahudawan sahyuniya, ta yadda wani babban jami'i a wannan masarauta da larabawa da musulmi suke kallonta da kima, ya buda baki ya kira masu kare kansu daga zaluncin Isra'ila a matsayin 'yan ta'adda.

A cikin 'yan makonnin da suka gabata, ministan harkokin wajen masarautar iyalan gidan Al Saud Adil Jubair ya furta cewa, nan ba da jimawa ba za su kwace makaman da ke hannun kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin palastinawa yan gwagwarmaya.

3514066

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
muhd lawan isyaku
0
0
Allah yasa kowa da kowa ya fahimta
captcha