IQNA

Ya Zama Wajibi Saudiyyah Ta Daina Daukar Nauyin “yan Ta’addan Daesh

23:57 - July 12, 2016
Lambar Labari: 3480605
Bangaren kasa da kasa, wani kwamitia majalisar dokokin kasar Birtaniya ya bukaci Saudiyyah da ta daina daukar nauyin kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Middle East Eye cewa, a jiya wani kwamitia majalisar dokokin kasar Birtaniya ya bukaci Saudiyyah da ta daina daukar nauyin kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ita da sauran kasashen larabawan ynkin tekun fasha.

Bayanin ya ce babu wani abu da yake boye ga kowa a halin yanzu kan cewa Saudiyya da wasu daga cikin kasashen larabawan yankin ne suke daukar nauyin yan ta’adda, musamman ma kungiyar daesh mafi hadari a duniya.

Wannan kira ya zo ne sakamakon irin karuwar ayyukan ta’addanci a kasashen da aka haifar da rikici wanda kuma yanzu ya fita daga kasashen har kasashen yammacin turai.

Shi dai wannan kwamiti ya dora alhakin zubar da jinin da ake na jama’a akan kasashen da suke daukar nauyin yan ta’addan ta hanyar bas u kudade da makamai da kuma horo, wanda kuma kasar Saudiyya it ace kan gaba ta wannan fuska.

Yanzu haka dai kungiyar ta Daesh ta fara amfani da wasu daga cikin makamai mafi hadari da gwamnatin Saudiyya ta saya musu daga Amurka, inda suka yi amfani da daya daga cikin domin kakkabo jirgin yaki.

Ta’addancin da ake fama da shi a halin yanzu kasashen larabawa wanda ya fara bazuwa har zuwa kasashen duniya, ya samo asali ne daga mummunar akidar nan ta kafirta al’ummar musulmi wadda ita kuma ta samo tushe daga akidar wahabiyanci, akidar da masarautar Saudiyya ta ginu a kanta.

3514555


captcha