Kamfanin dillancin labaran Iqn aya nakalto daga
shafin sadarwa na yanar gizo na yada labarai na Telesur ya bayar da rahoton
cewa, mahukunta a birnin Nice na kasar Faransa sun ce harin da wani mutum ya
kai a birnin a wancan mako da ya gabata ya shafi musulmi da dama, inda mutane
30 daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin musulmi ne, wasunsu
'yan kasashen Morrocco ne da Algeria da kuma Tunisia.
Usman Aisawi shi ne babban daraktan cibiyar musulmin wannan birnin, kuma limamin daya daga cikin manyan masallatan a garin, ya bayyana cewa abin da ya faru aiki ne na ta'addanci, kuma wannan mutum da ya aikata haka duk da kasancewarsa musulmi ne, amma ba ya wakiltar musulmi a cikinabin da ya aikata.
Ya kara da cewa daga cikin wadanda suka rasu akwai muuslmi da dama da suka hada da Fatima Charihi 'yar shekaru 60 da haihuwa 'yar kasar Morocco, wadda ta bar 'ya'ya 7 da ta haifa.
Malamin ya kirayi dukaknin al'ummar kasar da su san cewa musulunci ba addinin ta'addanci ba ne, hatta su kansu musulmi suna cikin barazanar 'yan ta'adda a kowane lokaci, kumata'addanci yana shafarsu kamar yadda kowa ya gani a harin nabirnin Nice, haka nan kuma da abin da ke faruwa a kasashen yankin gabas ta tsakiya, inda 'yan ta'adda suke kashe musulmi suna yi musu yankan rago a kasashen daban-daban.