IQNA

Daftarin Kudi Kan Sanin Mulsunci A Majalisar Dokokin Amurka

23:33 - August 01, 2016
Lambar Labari: 3480668
Bangaren kasa da kasa, an gabatar da wani daftarin kudiri domin dubi kan irin matsalolin da musulmi suke fuskanta a cikin kasar Amurka domin yin dubi kan haka.
Kamfanin dillancin labaran Iqn aya nakalto daga shafin sadarwa nan a PRNewswire cewa, Bill Cook dan majalisar dattijan Amurka ne daga jahar Califirnia ya bayyana cewa, wannan watan na Agusta watan sani muslunci ne.

Ya ce abubuwa da dama sun wakana wadanda ya kamata a zauna a yi karatun ta natsu a kansu dangane da musulmi, musamman a lokutan baya-bayan an da musulmi suke fuskantar tsangwama saboda ayyukan ta'addanci.

Dan maja;lisar ya ce a kan ya shirya daftarin kudiri mai taken watan Agusta watan sanin muslunci, wanda za a duba shi kuma a yi bahasi a kansa amajalisar dattijan kasar ta Amurka.

Ya ce babbar manufarsa ta gabatar da wannan daftarin kudiri it ace neman a yi adalci ga musulmi, domin kuwa an azaluntarsu ba tare da hakkinsu a fadin kasar, wanda hakan ya sabawa dimukradiya da kuma tsarin kasar Amurka da ma hakkin dan adam.

Cook ya kara da cewa, ya shirya daftarin kudirin ne bisa ga irin rahotanni da aka tattara da ke nuni da cewa, kyamar musulmi ta karu da kashi 58 cikin dari a kasar, a cikin shekarun 2014 da kuma 2015, da hakan ya hada da kai hare-haren da ake kan masallatai da wuraren ibadar msulmi da suke zaune da kowa lafya, bas u da wata alka da yan ta'adda.

3519174

captcha