Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa
ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, rahotanni daga kasar ta
Pakistan sun ce an gudanar da wanann zama ne a cikin gundumar Baluchestan, tare
da halartar wasu daga cikin fitattun malamai na bangarorin sunna da shi'a na
yankin da ma wasu yankuna na kasar ta Pakistan, da nufin karfafa fahimtar juna
da kuma yaki da mummunar akidar nan ta kafirta musulmi, wadda ita ce tushen
ta'addanci a halin yanzu a cikin kasashen musulmi.
Daga cikin malaman da suka halarci taron akwai Maulana Shirani, shugaban majalisar malaman sunnah a yankin Baluchestan, da kuma Sayyid Hashim Musawi, daya daga cikin manyan malaman shi'a na kasar Pakistan, kuma limamin birnin Birnin Kuita na mabiya mazhabar shi'a, gami da wakilan sauran kungiyoyin 'yan sunnah na kasar, da suka hada da 'yan salafiyyah, Jama'at Ahlu Hadis da sauransu.
Dukkanin wadanda suka halarci taron sun nuna farin cikinsu dangane da yadda taron ya gudana a cikin yanayi na 'yan uwantaka ta muslunci da girmama juna, kamar yadda kuma mahalrta taron suka bukaci da a sake farfado da kungiyar hadin kan musulmi ta kasar Pakistan wato Millat Islamiyyah Mahaz, wadda ta hada wakilan dukkanin bangarorin musulmin kasar, da suka hada da 'yan sunnah, da shi'a da kuma darikun sufaye.
Bayan kammala taron a yammacin jiya, Maulana Shirani ya jagoranci sallar Magariba wadda ta hada dukkanin bangarorin kungiyoyin musulmi da suka halarci taron.