Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarat cewa, ya nakalto daga shafin labarai na alyaoum24.com cewa, an gudanar
da taron Liksa karo na goma a birnin Alaraish na kasar Morocco, inda aka nuna
fina-finai da kuma hotuna, yayin da mawaka suka gabatar da wakokinsu asu kuma
har da mata suna rawa, inda wasu suka nuna rashina mincewa da abin da aka yi.
Alqazabri ya ce a wurin taron wasu sun rika yin izgili da ayoyin kur'ani mai tsarki, inda aka rika karanta ayoyin littafin mai tsarki mata suna rawa tsirra suna rerawa, wanda acewasa hakan ya sabawa ala'dun muuslmi na kasar Morocco, kuma ba za su taba yarda da hakan ba.
Ya ce wannan birnin na Alaraish yan adaga cikin birane da suka tashi a cikin muslunci kuam suke da tarihi na addini da kyawawan dabiu na muslunci, saboda haka gudanar da wannan taroa acikinsa da kuma irin abubuwan da aka yi ba badaa da shashanci ya sabawa koyarwar muslunci.
Wannan taro dai yana daga cikin tarukan da ake gudanarwa a kasar ta Moroccoa cikin gundumar kazablanka yau kimanin shekaru goma a jere, wanda yake samu halartar matasa daga sassan kasar da ma wasu kasashe na duniya, amma a wannan karon ana ganin cewa abin da aka yi a taro ya wuce kima.