Kamfanin
dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar
gizo na «Syracuse.com» cewa, an kori wata
musulma ‘yar shekaru 32 ba'amurka tare da cin zarafinta a cikin wata cibiyar
kasuwanci a Jahar Texas ta Amurka, a lokacin da ta je yin sayayya bayan da ta
saka hijabin mulsunci.
Sara Safi wadda ‘yar asalin India ce ta bayyana mamakinta matuka dangane da yadda wasu Amurkawa suke kallon musulmi, domin hakan ya sabawa dukkanin dokokin kasar, kamar yadda kuma ya sabawa yan adamtaka.
A lokacin da matar take yin sayayya wani daga mutanen da suke karbar kudade y ace da it aba zai sayar mata da kayan ba har sai ta cire hijabin da ake akanta, ko kuma ta fita daga wurin ko kuma ya kira mata yan sanda, wato yana mai nufin cewa zai ja mata wani sharri a wurin.
Ganin haka ta fice daga wurin, amma daga bisani ta bayyana ma masu kula da wurin abin da ya faru, inda aka duba kamara da ke daukar hutunan dukanin abin da yake faruwa a cikin kasuwar, kuma ak atabbatar da abin da ta fada.
To sai dai abin jira again shi ne wane irin mataki ne za a dauka kan wannan mutum domin ladabtar da shi, domin sau tari abubuwa irin hak suna faruwa na cin zarafin musulmi, ko da an kai kara sai a wawantar da maganar.