IQNA

An Gudanar Da Taron Maulidin Fatimah Ma'asuma (SA) A Sweden Da Hamburg

23:32 - August 05, 2016
Lambar Labari: 3480678
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da tarukan maulidin Sayyidah Fatima Ma'asumah (SA) a kasashen Sweden da kuma Jamus.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar Imam Ali (AS) da ke birnin Stockholm na kasar Sewden cewa, an gudanar da taron ne a masalalcin cibiyar Imam Ali (AS) inda Mohsen Hakim Ilahi ya gabatar da jawabi.

Da kimanin karfe 19 na dare ne aka fara gudanar da taron, wanda kuma ya samu halartar mutane da dama.

A can birnin Hamburg na kasar Jamus ma an gudanar da irin wannan taro mai albarka na tunawa ranar zagayowar haihuwar Sayyida Fatima Ma'asuma (sA) tae da halartar mabiya tafarkin iyalan gidan manzo.

Ayatollah Ramezani ne dai ya gabatar da jawabi a wurin, tare da halartar jama'a da dama, inda ya yi bayani kan matsayin wannan baiwar Allah da kuma darussan da suke kunshe a cikin rayuwarta mai albarka.

captcha