Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na
jaridar Raya cewa, Na'ima Wahabi Sultan yar shekaru 85 wadda ta hardace kur'ani
kwanan baki dayansa ba ta da ilimin rubutu ko karatu ga yawan shekarunta, amma duk da haka saboda
kwazonta ta hardace kur'ani mai tsarki.
Bayanin ya ce an haife ta a cikin shekara ta 1931 a cikin birnin Khalil, kuma ta rayu na tsawon shekaru ba tare da masaniya kan kur'ani ba saboda halin da aka jefa al'ummar yankin.
Daga bisani tana ganin yadda ake koyar da yara a wani wurin koyar da karatun kur'ani, wannan ya burge ta wanda kuma hakan ya sanya ta shiga ita ana koyar da ita, kuma cikin ikon Allah ta samu nasarar hardace kur'ani baki daya.
Wanann mata ta yi nasiha ga matasa da su mike wajen koyon kur'ani mai tsarki da kuma ilmominsa, wanda hakan zai basu damar su gina rayuwarsu a kan koyarwa ta wannan littafi mai tsarki a matsayinsu na 'ya'yan musulmi.