Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin jaridar The Nation cewa, sarkin musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar ya yi kira da a rika bayar da ‘yancin yin addini yadda ya kamata a kasar ba tare da tauye wa wani dan Najeriya hakkinsa na yin addini da yake so ba.
Sarkin ya bayyana hakan ne dangane da matsalolin da aka ta samu a kasar, inda wasu jahohi suka nemi fakewa da batun tsaro domin hana mata musulmi saka hijabi, da sunan suna daukar matakan tsaro, inda ya bayyana hakan da cewa bas hi ne mafita, domin saka hijabi a wurin mata msuulmi Magana ce ta addini.
Ya kara da cewa bababn abin da ake bukata a kasar shi ne kara samun fahimtar juna da hadin kai a tsakanin dukkanin al’ummominta da kabilunta da mabiya addinai kasar, wanda hakan zai kara taimakawa wajen samun kasa guda mai zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummarta.
Haka nan kumaya yi kira da mutane su zama masu hakuri da kiyaye kaidoji da girmama akidar kowa, tare da rashin yin shigar shugula a cikin harkokin da bas u shafi mutm ba, hakan ne zai sanya a zauna lafiya.
Dangane da jahohin da suka yi hankoron hana mata musulmi saka hijabi sabon batun tsaro kuwa, sarkin ya yi da a sake yin nazarin kan lamarin domin kada a tauye ma wani bangare na al’ummar kasar hakkinsa.