Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cwa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Dunya Bultini cewa, adadi mai yawa na mata musulmi suna zuwa wannan cibiya da aka ude domin koyar da kur’ani a cikin yankin Kousseri.
Wata cibiya ce da take gudanar da ayyukan jin kai da hakan ya hada da gina makarantu da kuma samar da guraben ayyukan yi gwargwadon iko ga mutane mabukata, ita ce ta dauki nauyin gudanar d wannan aiki.
Khadija Liman tana daya daga cikin malamai da suke koyar da mata karatun kur’ania wannan cibiya, ta bayyana cewa hakika wannan babban ci gaba ne suka samu a wannan kauye, inda baya ga koyar da karatun kur’an, suna koyar da rubutu da karatu ga mata wadanda ba su taba yin makaranta ba.
Tun kafin wannan lokacin da akwai makarantu da na koyar da karatun ur’ani a wasu yankunan kasa musamma ma dai manyan biran, amma kauyuka ne suka fi fuskantar matsaloli ta wannan fuska.
Safa Narli na daga cikin wadada suke aiwata da wannan shiri ta bayyana cewa, suna burin ganin wanna shiri da suka fara aiwatarwa a karkara guda acikin kasar kamaru ya bunkasa zuwa sauran yankunan da ba su samu irin wannan dama ba.
Kamasr Kama dai na daga cikin kasashen Afirka da suke da mabiya addinai na musulunci da kiristanci, kuma al’ummar kasar suna zaun da junansu lafiya ba tare da wani tashin hankali ko rashin fahimtar juna ba, wanda hakan ya zama babban abin buga misali da shi.