Inda shi kuma ya bayyana duk mutumin da ke adawa da shirin kasarsa na fadada yankinta zuwa yankin Palasdinawa, da mai marawa kokarin kawar da wani jinsi daga ban kasa.
Mista Ban Ki-Moon ya bayyana kalaman fira ministan Isra’ila da cewa kalamai masu matukar sosa rai.
Ya kuma ce ya kamata ya sani cewa shirin fadada girman Isra'ila haramtacce ne.
Sai dai kuma wannan na zuwa ne watanni kadan kafin Mista Ban Ki-Moon ya bar ofis, a karshen wannan shekarar.