Cibyar ta Imam Ali (AS) dai an daga cikin cibiyoyin musulunci mafi girma a cikin nahiyar turai da suke gudanar da harkoki na addini a kasar.
Daga cikin ayyukanta kuwa har da gudanar da tarukan na tunawa ranaku na haihuwa ko shahadar limamai daga cikin iyalan gidan manzo, da kuma wasu daga cikin tarukan musulunci.
Tun a cikin watan Yunin shekara ta 2001 ce da aka bude wannan babbar cibiya ta Imam Ali (AS) a hukumance a birnin Vienna.
A ya ne 20 ga watan zul hijja ake gudanar da taron maulidin Imam Kazim (AS) a wannan cibiya tare da halartar daruruwan musulmi.